Bangaren koyon na'ura mai ƙwaƙwalwa, MARKAZ tana kokarin samar da dakin koyar da na'ura mai ƙwaƙwalwa don koyar da yara abubuwa masu muhimmanci da suka shafi Computer, wannan yunkuri da Markaz ta samar zai bawa yara damar koyon abubuwa masu amfani da taimaka musu a wannan duniyar da muke ciki ta yanzu da ta koma ta zamanin na'ura mai ƙwaƙwalwa, kasashe da makarantu da suka ci-gaba, sun samar da irin wannan yanayi.
Dakin Karatun Markaz wato Library, inda muke da tsarin littattafai na karatu tare da samar da pdf online ga Daluban mu da bada iya mallakar littafi.
Dakunan karatun Markaz ga daliban kwana, wuri kamar gida, tare da kulawa na musamman ga kowane dalibi, tsaftacen wuri, kulawa da lafiya.
Wurin duba lafiyar dalibai .
Markaz tana wuri mai cike da tsaro da kulawa sosai na mutane da hukumomi. Babu fargaban tsoro ko tsaro a wurin, domin kuwa muna da tsaro mai karfi a wurin.
Azuzuwa Na zamani na karatu, tare da dukkan kayan karatu da ake bukata.
Azuzuwan Karatu na Online cikin sauqi da sauƙaƙawa, hanya mafi kyau , sauƙin network, rashin shan data.
Wadataccen fili don ayyukan makaranta, da wuri mai kyau ga dalibai don gudanar da ayyukan makaranta, kamar taro, musaffa, da sauran su.
Markaz tana da sha'awar samar da wuraren Wasanni da buda ƙwaƙwalwa saboda yara, mun fahimci muhimmancin wasa da karatu a wurin yara, siyasa muke da tsarin samar da gasa ta ilimi, Wasanni na ilimi don habbaka kuzari da tunanin su.