Markazu Riyadil Jannah Makaranta ce wacce ta Shahara sosai wajen karantar da fannonin ilimi daban - daban a zahiri harma Dana online domin saukakawa Dalibai na Kusa Dana nesa ta yadda dubban dalibai suke samun Damar yin karatu daga sassa daban daban Kuma ba tare da sun biya ko sisi ba.
Sannan Makarantar tana da register da CAC (Gwamnati), Kuma Makaranta ce wacce take da manufofi da tsarurruka Masu matukar kyau domin kawo sauyi Mai kyau a bangaren karantarwa na Addini dama na zamani domin anfanin Musulunci da Musulmi gaba daya.
Daga cikin Manufofin akwai Tsari da Manufa ta Gina...
1-Masallaci na Jumu'a
2-Makarantar Haddar Qur'ani (Tahfeez)
3-University (Jami'a)
4-Asibiti
5-Gidan TV
Da Sauransu