FARA KARATU
MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY
FANNIN ARABIYYA
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
“Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri, sai ya fahimtar da shi addini”. [BUKHARI DA MUSLIM]
Ya ku 'yan'uwa/'yar'uwa, daluban shirin Markaz Academy
Salati da rahama da amincin Allah su tabbata a gare ku. Bayan haka:
Muna shaida muku cewar in shaa Allahu Ranar Litinin mai zuwa zamu cigaba da ɗora muku darussan ku a azuzuwanku na Telegram in shaa Allah.
Wanda suka yi Term payment bayananku suna tare da mu, kuma zaayi muku approving domin shiga kai tsaye cikin App din Markaz don cigaba da ayyukan karatu da makaranta. Amma duk wanda ya biya ya tabbatar da ya turo shaidar biya.
Duk wasu wajib, aiki, test, jarabawa, Attendance zasu gudana ne ta wannan App din da muka bada. Nasan zaku dinga ganin saqonni ta email dinku. Shiyasa yake da muhimmanci ayi payment.
Ga wanda Markaz ta cire su ko ta dakatar saboda laifin rashin Iktibar, munce zasu iya komawa ta link din da muka bada su sake sabon registration daga Farko, zaayi musu approving a basu Aji da izinin Allah.
Allah ya gafarta mana laifukan mu
MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY
16/07/2025